Fayose ya bijire wa umarnin PDP, ya kaddamar da neman takarar shugaban kasa

0

Duk da umarnin da jam’iyyar PDP ta bai wa Gwamnan Ekiti, Ayo Fayose cewa kada ya bata lokacin sa neman takarar shugabancinn kasa a 2019, gwamnan ya kadaddamar da kan sa a yau Alhamis, a otal din Chelsea da ke Abuja.

Ya yi kaddamarwar duk kuwa da cewa an rigaya jam’iyyar ta ce sai dan Arewa ne zai tsaya mata takarar shugaban kasa a 2019.

Jihar Ekiti dai ta na yankin Kudu maso yammacin Nijeriya ne, ba yankin Arewa ba.

Share.

game da Author