An kammala jigilan mahajjatan jihar Kaduna daga kasar Saudiyya

0

Jami’in kula da harka da jama’a na hukumar kula da jindadin mahajjata na jihar Kaduna Yunusa Abdulahi ya sanar da cewa an kammala jigilan mahajjatan jihar daga kasar Saudi.

Yunusa ya ce mahajjata 6,713 ne suka tafi aikin haji bana daga jihar Kaduna wanda hudu daga ciki suka rasu a Makkah.

” Kamfanin jirgin saman Medview ne ta sauke sauran ragowan mahajjata 212 da misalin karfe 7:05 na safiyar Alhamis”

Ya kuma kara da cewa a shekaran bana kamfanonin jiragen saman Medview da Max Air ne suka yi jigilan mahajjatan daga kasar Saudi zuwa Kaduna.

Share.

game da Author