Kotun karan dake Iyaganku jihar Oyo ta gurfanar da wani magidanci mai suna Samson Ayodele da ta kama da laifin aikata fiyade ga wata yarinya ‘yar shekara 12 a dakinsa.
Wanda ya shigar da karan Folake Ewe ya fada wa kotun cewa Samson ya aikata hakan ne ranar 18 ga watan Satumba da misalin karfe 2 na rana.
Ya ce Samson ya zolayi yarinyar ne har ya kai ta dakinsa dake Adeyi Avenue Bodija Ibadan sannan ya danne ta da karfin tsiya.
Alkalin kotun I.O.Olanipekun ya yanke hukuncin daure Samson a kurkuku har sai bayan ya saurari shawarwari daga bangaren da ake gurfanar da mutane masu aikata irin hakan.
Alkalin ya kuma daga sauraron karan zuwa 19 ga watan Oktoba.