AMBALIYA: Rundunar Sojin saman Najeriya ta kai gudunmawar magunguna sansanoni a jihar Benue

0

Rundunar sojin saman Najeriya ta tallafa da magunguna kyauta ga mazauna sansanonin da ambaliyar ruwa ta shafa da suka kai 600 a jihar Benue.

Shugaban fannin kiwon lafiya na rundunar sojin saman Jeremiah Amase ya sanar da hakan wa kamfanin dallanci labaran Najeriya yau Litini.

Ya ce ma’aikatan kiwon lafiyan su suna kula da mutanen da suka kamu da cututtuka kamar su zazzabin cizon sauro, hawan jini,amai da gudawa,cutar dake kama hakarkari da sauransu.

Jeremiah Amase ya kara da cewa a yanzu haka mutanen sun fara samun sauki.

Rundunar Sojin sama ta hada guiwa ne da gwamnatin jihar Benue, asusun UNICEF da sauran kungiyoyin bada tallafi na ciki da wajen kasar domin agaza wa mutanen da ambaliyar yayi wa hasara.

Share.

game da Author