An kama wani mutum da laifin yin lalata da wata yar shekara 4 a jihar Neja

0

Wani mutum mai shekaru 34, Ahmadu Musa, ya yi ikirarin cewa shi fa sau daya tal ya san ya taba yin lalata da wata karamar yarinya ‘yar shekara hudu da haihuwa.

Ahmadu ya yi wannan ikirari ne a gaban Kungiyar Kare Hakkin Kananan Yara, ta Jihar Neja, a ranar Litinin.

Musa, wanda mazaunin kasuwar New Market ne da ke kusa da Kasuwar Gwari, cikin Karamar Hukumar Chanchaga, ya ce shi sau daya ya yi lalata da yarinyar, amma ba zai iya tuna kwanan wata da ranar da hakan ta faru ba.

“Kawai na gan ta ne ta na wucewa ta kofar gida na, sai na kira ta, na ce ta zo ta sayo min ‘pure water’. Daga nan sai na ribbace ta, har na yi lalata da ita.

“A karo na biyu na kira ta cikin wani kango, na fara cire wando na kenan da shirin yin fitsari kafin na yi lalata da ita, sai aka kama ni.” Inji Ahmadu Musa.

Shi kuwa Shugaban Kwamitin Kwaya da Laifuka Haram ne, Abdulmumin Aliyu, wanda shi ne ya kama wanda ake zargin, ya ce Musa kekesasshiyar zuciyar aikata laifuka gare shi, kuma ba tuba ya ke yi ba, domin an sha kama shi dumu-dumu cikin aikata munanan laifuka a baya.

“An sha kama Musa ba sau daya ba, kuma ya sha dauri a kurkuku sau da dama, amma da ya fito sai ungulu ta koma gidan ta na tsamiya.” Inji Aliyu

“Yau dai karyar sa ta kare, lokacin da muka kama shi. Ya kira yarinyar ne kamar za ta sayo masa pure water, sai ya ja ta zuwa cikin wani kango da nufin sake yin lalata da ita.

“Cikin ikon Allah sai wani mutumin kirki ya gan shi, inda nan da nan, ya ihun neman gudummawa, aka cafke shi.

Matan unguwa su ka taru, suka lakada masa dukan tsiya.

“Ba don Allah ya kai mutanen mu da wurin ba, da matan makwabta sun kashe shi.

Babbar Daraktan Kungiyar Kare Hakkin Kananan Yara, Mairam Kolo, ta ce kungiyar su za ta bi diddgin laifin da Musa ya aikata domin tabbatar da cewa an hukunta shi.

Share.

game da Author