Rashin biyan albashi da kudaden fansho a jihohi na ci min Tuwo a kwarya – Inji Buhari

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya nuna fushin sa dangane da yadda Gwamnonin Jihohin kasar nan ke kashe kudaden Paris Club da Gwamnatin Tarayya ta rika ba su, domin toshe barakar matsaloli.

Buhari ya nuna wannan fushin ne ranar Litinin yayin da ya ke taro da Majalisar Sarakunan Gargajiya na Najeriya, a fadar gwamnati.

A cikin watan Mayu ne dai gwamnatin tarayya ta fitar da jadawalin kudaden da ta ba jihohi daga cikin kaso na biyu na Paris Club, wadanda adadin su ya kai naira biliyan 243.7.

Shugaban ya ce abin takaici ne matuka a ce har akwai gwamnonin da za su kasa biyan ma’aikatan jihar su hakkokin su kamar kudaden ritaya, albashi da fansho daga cikin kudin Paris Club da ake ba su.

“Na saki batun da ya tara ku a nan, na shiga wani batun daban. Dalili, saboda ina so na gamsar da ku cewa a kullum ina kwana da tashi cikin matsalolin da ke dabaibaye da kasar nan, yawancin su kuwa duk wadanda su ka shafi talakawa ne.”

“Akwai ma’aikatan da sun kai wata shida ba a biya su albashi ba, akwai kuma ma’aikatan da su ka shafe shekaru da yin ritaya amma har yau ba a biya su kudaden sallamar su ba.”

“Ina kira ga gwamnoni da su gaggauta biyan ma’aikata hakkokin su, saboda yawancin su da wadannan kudaden ne su ka dogara su biya haya da kuma kudin makarantar ‘ya’yan su.”

A karshe kuma ya sha alwashin wannan gwamnati za ta ci gaba da aiwatar da ayyukan ci gaban al’umma domin inganta rayuwar ‘yan Nijeriya a kowane bangaren kasar nan.

Share.

game da Author