‘Yan sanda a jihar Ogun sun cafke wani mutum mai shekaru 32 da ake zargin ya daki makwabcin sa da guru da layu ya mutu.
Mutumin da ake zargi mai suna Olatunda Okapo, ya daki makwabcin sa mai shekara 42 ne a kauyen Alapako-Eke, da ke cikin Karamar Hukumar Ido.
Rundunar ‘yan sanda ta bada sunan mamacin August in Ode, inda ta ce an kama wanda ake zargin ne bayan dan uwan mamakin ya kai rahoton abin da ya auku.
Sun ce dan uwan wanda aka dokan din ya shaida wa ‘yan sanda cewa sabani ya shiga tsakanin wanda ya yi duka da kuma wanda aka doka, Daga baya abin ya kai su ga rukumewa da fada.
Ya ce daga nan sai Olatunde ya garzaya daji ya dauko wani guru, ya na fitowa ya doki Ode da shi, nan take ya fadi ya mutu.
‘Yan sanda cewa an kai gawar mamacin asibiti, aka tabbatar da mutuwar sa. Su kuma su na tsare da wanda ake zargin da su ka ce za su gurfanar da shi a kotu.