An gurfanar da wata mata a kotu saboda ta kira uwar mijinta mayya

0

Kotu a garin Minna, jihar Neja ta roki wasu mata biyu da su sasanta kansu bayan uwar tsohuwar mijin Fatima Mohammed ta roki Kotu da ta sa tsohowar matan danta ta biya ta naira miliyan 2 saboda kiranta mayya da tayi don taki maida mata da danta da ya zo hutu.

Fati Mohammed ta yiwa Uwar mijinta Fati Aliyu lakabi da maita.

Kotu ta roki matan biyu da su je su sasanta kansu mai makon tonon silili da syke yi wa juna a kotu.

Shi dai yaron ya tafi gidan uwar sa ne hutu inda daga nan ita uwar taki maida shi wajen kakarsa inda ubansa ya ajiye shi bayan sun rabu da uwar.

Share.

game da Author