Yau Shugaba Buhari zai dawo Najeriya

0

A yanzu haka Shugaba Muhammadu Buhari na kan hanyar sa ta dawowa gida Najeriya daga Birnin Ladan.

Wata sanarwa daga Kakakin Shugaban, Femi Adesina, ta bayyana cewa Buhari zai dawo yau Asabar, kuma zai yi wa al’ummar Najeriya jawabi a ranar Litinin.

Sanarwar ta ce ya gode wa daukacin jama’a dangane da addu’o’i da goyon baya da ake bai wa gwamnatin sa.

Buhari ya bar Nijeriya ne tun ranar 7 Ga Mayu, 2017.

PREMIUM TIMES Hausa ta tabbatar da cewa tuni jirgin da ke dauke da shi ya baro Landan, ya kamo hanyar Abuja.

Share.

game da Author