Ibtila’in fyade ga ‘yan mata na neman ya addabi mutanen Jihar Filato

0

Kakakin rundunar ‘yan sandar jihar Filato Terna Tyopev ya yi kira ga iyaye musamman wadanda ke da yara kanana mata da su tabbata suna sa ido ga ‘ya’yansu wajen kula da wuraren da suke aiken su da inda yaran ke zuwa.

Terna ya fadi haka ne ganin yadda fyade ke neman ya zama ruwan dare a jihar.

Ya ce a cikin watanni biyu da suka wuce an kawo kararraki da ya shafi yi wa mata fyade da ya kai 20 ofishin yan sandan.

Daga karshe Terna Topev ya ce rundunar yan sandan na kira ga iyaye da su kara sa wa ya’yansu idanu domin kubuta daga wannan bala’I da ke neman ya gagari jama’.

Share.

game da Author