Jagorar kwamitin da zai kula da kiwon lafiyar mahajjata a kasar Saudiyya na kasa Ibrahim Kana ya fadi wasu hanyoyi da mahajjaci zai bi don yin aikin haji cikin koshin lafiya a kasa mai tsarki.
Ibrahim Kana ya sanar da wannan gidan jarida PREMIUM TIMES kokarin da suka yi da irin shirye-shiryen da hukumar NAHCON ta yi don samarwa mahajjatan Najeriya ingantacciyar Kiwon lafiya.
“Hukumar NAHCON ta dauki kwararrun ma’aikatan kiwon lafiya da suka kai 400 wanda za su kula da marasa lafiya a kasar Saudi da ma’aikatan ‘duba gari’ da za su zauna da mahajjatan suna wayar musu da kai kan muhimmancin tsaftace mazauninsu domin guje wa kamuwa da cututtuka sannan kuma mun samar da na’urorin aikin asibiti na zamani a asibitocin mu da ke Makkah da Madina domin samun sauki ga aiyukkan mu na kula da kiwon lafiyar mahajjatan.
“ Muna da kyakkawar fahimta tsakanin mu da kasar Saudiyya domin kafin a fara tashi zuwa aikin haji bana sakatariyar hukumar mu Binta Adamu Bello ta gana da ministan kiwon lafiyar kasar Saudi a Riyadh inda kasar ta amince ta kara yawan cibiyoyin kiwon lafiya a kusa da masallacin Annabi Muhammad S.A.W da karban marasa lafiyar mu koda cutar ta gagari namu likitocin.
“A yanzu haka koda aikin fida ne mutanen mu za su bukata asibitocin Saudi za su yi.
Da aka tambayeshi game da shirin da kasa Najeriya ta yi na wadata asibitocin ta da magunguna da kayayyakin aiki, Ibrahim ya zayyano wasu matsaloli da hukumar ke fama su musamman wadanda suka shafi mahajjata.
“ Matsalolin da muka fi fuskanta a wannan fannin sune rashin sani da horo. Misali mafi yawan mutanen Najeriya na zuwa asibiti domin karban magunguna kyauta ba don suna bukata ba. Ina kira ga mutanen mu idan ba ya zama dole ba a daina zuwa asibiti domin karban magani haka kawai domin hakan na kawo mana matsalar gaske.
Bayan haka yayi kira ga mahajjata da su tabbatar sun yi alluran rigakafin da ya kamata musamman na cututtukan sankarau, cutar zazzabin cizon sauro da makamantan su sannan yace “duk macen da ke da ciki dama baza mu dauke ta ba.”
“Masu cutar hawan jini,cutar siga su tabbatar sun sami izinin tafiya daga wajen likitocinsu, masu cutar kanjamau basu da matsalar domin ministan kiwon lafiya ya samar musu da isassun magungunan cutar da za su bukata.
Da ya ke bayani akan matsalolin da akan fuskanta musamman idan an fita aiki ko ziyara a kasar, Ibrahim yayi kira ga mahajjata da su yawaita rike ruwan sha tare da su.
“ Babbar matsalar da aka fi samu shine yawan suma saboda tsananin zafi. Shawarata shine mahajjata su tabbatar suna rike da ruwan sha kowani lokaci, su rike tufafi marasa nauyi sannan su rage zama inda mutane suka yi cinkoso.
“Bayan haka shugaban NAHCON ya hada hannu da ministan kiwon lafiya Isaac Adewole wajen aikawa da kwararrun ma’aikatan kiwon lafiya wanda za su gaggauta bada kula ga marasa lafiya a Madina. A yanzu hakan ma wasu ma’aikatan na aiki a Madina.
Daga karshe Ibrahim Kana ya yi kira ga mahajjata da su guji cin abinci kai tsaya ba tare da kula da tsaftarsa ba.
“ Shawaran da zan bada shine mahajjata su guji siyan abincin masu tallan da ba su tabbatar da tsaftan ta ba, su tabbatar abincin da za su ci yana da tsafta sannan ina kira ga ma’aikatan da su yi amfani da motocin daukan marasa lafiya wato ‘Ambulances’ta hanyar da ya kamata.
“Asibitocin mu a Makkah da Madina bude suke kowani lokaci.”