Matan da ke dauke da cutar kanjamau za su iya shayar da ‘ya’yansu nono

0

Shugaban hukumar kula da gudanar da bincike kan garkuwar jikin mutum na Najeriya Alash’le Abimiku ya ce da taimakon magungunan cutar kanjamau matan da ke dauke da cutar za su iya shayar da ‘ya’yansu ruwan nono har na tsawon watanni shida.

Ya fadi haka ne yayin da kamfanin dillancin labaran Najeriya ta yi hira da shi.

Ya fadi cewa kamata ya yi macen da ke dauke da cutar kanjamau ta juri shan magungunan cutar domin haka ne kadai zai kubutar da jaririn ta daga kamuwa da cutar a lokacin da yake ciki, lokacin haihuwa da kuma lokacin shayarwa.

Ya ce bayan haihuwa jaririn zai dinga shan wani magani wanda ake kira da ‘prophylaxis’ na tsawon makoni shida wanda zai kara kare jaririn daga kamuwa da cutar ta hanyar shan nonon mahaifiyar sa.

Alash’le ya ce ruwan nono na bunkasa garkuwan jikin jaririn sannan ta hakan mahaifiyar za ta iya rage kiban da ta samu a lokacin da take da ciki.

Share.

game da Author