Ya zama wajibi mu tabbatar da yin nasara -Cewar Osinbajo

0

Mukaddashin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya shaida wa ministoci cewa ya fa zama wajibi su tabbatar da cewa sun kai ga samun nasara wajen kalubatantar tattalin arzikin kasar nan.

Osinbajo ya yi wannan jawabi ne a rananr Alhamis, yayin taron Majalisar Zartaswa a fadar Aso Rock, cikin Villa.

Ya yi wannan jan-hankali ne a yayin bude taron ministoci a kan Shirin Farfado da Tattalin Arzikin Kasa da aka fara a fadar shugaban kasa.

Mukaddashin Shugaban Kasan ya ce yanzu ne aka fara gagarimin shirin farfado da tattalin arzikin ka’in-da-na’in.

“Ya kamata mu sakankance wa kan mu, mu yarda cewa babu wani abu da zai iya gagarar mu aiwatarwa a Najeriya. Saboda kamar yadda muka sani, a duniya samun nasara da kuma kasawa abu ne na kudirtawa a duniya. Idan ka kudirta nasara, to tabbas za ka samu nasara. Haka idan ka kawo kasawa a zuciyar ka, to ba za ka iya nasara ba.”

Wannan taro dai ya samu halartar manyan baki da dama, har da babban mai jawabi, Idris Jala, wani tsohon ma’aikacin gwamnatin Malaysia, wanda yay i jawabin da ya ratsa jinni da jijiyoyin mahalarta taron.

Da ya ke sharhi kan laccar sa, Osinbajo ya ce jawabin Mista Jala wani tsimi ne da ya kawo wa ‘yan Najeriya daga Malaysia, wanda idan mu ka sha shi, to za mu murmure, mu kuma wartsake, irin wartsakewa daga matsin tattalin arziki da kasar Malaysia ta yi a shekarun baya.

“Ni dai jawabin nan kalubale ne gare ni kankin kai na. Kuma na san cewa duk wani da ke nan an tsima jikin sa da wannan jawabin.” Inji Osinbajo, wanda ya kara da cewa abin da ya rage mana, kawai shi ne mu tabbatar cewa mun yi aiki da abin da mu ka saurara.

Share.

game da Author