Zaman dar-dar a Maiduguri bayan sojoji sun kutsa kai cikin ginin Majalisar Dinkin Duniya

0

Mazauna Maiduguri, babban birnin Jihar Barno sun tashi a safiyar Juma’a a cikin zaman dar-dar, bayan sojojin Nijariya sun kutsa kai cikin wani gini na Majalisar Dinkin Duniya.

Binciken da PREMIUM TIMES ta gudanar ya tabbatar da cewa sojojin sun afka cikin ginin ne a bisa zargin cewa wasu jami’an majalisar na yin sumogal din muggan makamai cikin ginin.

Ginin wanda sojojin su ka mamaye, wanda aka fi sani da suna Red Roof, shi ne ginin da Majalisar Dinkin Duniya ke amfani da shi wajen saukar jami’an ta. Ginin dai mallakar tsohon gwamnan jihar Barno ne, Mala Kachalla.

Wata majiya wadda ke da masaniyar kutsawa a cikin ginin, ta ce sojojin Nijeriya sun kai farmaki a ginin ne a bisa wani labari da jami’an tsaron sirri, SSS su ka yi musu, cewa sun fahimci akwai wata harkalla a cikin ginin, domin su kan ga wasu na wata zirga-zirga a cikin ginin da ba su yarda da su ba.

Ginin dai mai tsadar gaske ne, kuma a kewaye ya ke da doguwar katanta.

Sojoji sun kewaye ginin wajen karfe biyu na dare, sannan kuma su ka yi shinge a kan duk wata hanya mai shiga ko mai bullewa daga katafaren ginin.

Wata majiya da ta nemi a boye sunanta, ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa wannan rudani ya sa tuni Majalisar Dinkin Duniya ta dakatar da ayyukan jin kai da ta ke yi a jihar Barno.

‘‘Sojojin sun zo wajen karfe biyu na dare, suka zagaye dukkan wurin, sannan kuma wajen karfe uku na dare, suka nemi a ba su iznin shiga ciki.

“Amma sai jami’an Majalisar Dinkin Duniya su ka ce ce ba su yarda ba, domin yin hakan ya saba wa ka’idar majalisar, musamman a wannan lokaci na talatainin dare.

Sojojin dai wani Kanar ne ya yi musu jagora, sun ce sun samu labari daga jami’an SSS cewa ana shigo da muggan makamai cikin ginin Majalisar, a cikin wasu manya-manyan akwatuna na katakai.

“Mu kuwa mun san cewa babu wani abu mai kama da haka, saboda kwantinonin da ake shigowa da su duk kayan gini ne, wanda Majalisar Dinkin Duniya ke amfani da su wajen yi wa ginin kwaskwarima.

Haka majiyar ta shaida, sannan kuma ta kara da cewa a yanzu wannan ginin shi ne wurin kwanan jami’an MajalisarDinkin Duniya masu ayyukan jinkai a Maiduguri.

“Yayin da sojoji su ka nemi kutsawa a cikin gidan, sai masu gadi su ka yi wuf, su ka garkame kofar shiga ciki.

Majiyar kuma ta kara da cewa masu tsaron kofar da kuma sojojin sun kai har karfe bakwai na safiyar Juma’a su na cacar baki, kafin daga bisani aka ba su kofa su ka shiga ciki.

“Haka su ka shiga su ka bincike ko’ina a cikin gidan, amma ba u samu komai ba. Wajen karfe 7:45 na safe, su ka fice, su ka yi tafiyar su.

Sojojin dai sun shiga gidan ne a daidai lokacin da ake ta yada jita-jitar cewa shugaban Boko Haram Abubakar Shekau na cikin gidan sun boye shi.

PREMIUM TIMES ta isa wurin karfe 7:45 daidai na safe, a lokacin da sojojin su ka bada baya su ke tafiyar su.

Wani shugaban wata kungiya mai zaman kanta, Ahmed Shehu, wanda ya isa wurin kuma iske PREMIUMT TIMES a can, ya shaida cewa za su bincika su gano hakikanin abin da ya haifar da wannan kiki-kaka tsakanin sojojin Najeriya a kuma Majalisar Dinkin duniya.

Kokarin jin ta bakin kakakin yada labaran sojoji a Maiduguri, Onyema Okechukwu ya ci tura, domin wayar sa a kashe ta ke.

Shi ma kakakin jami’an Majalisar Dinkin Duniya a Maiduguri, Rabi’u Musa, ya tabbatar da faruwar lamarin, amma bai yi wani bayani ba. Ya dai yi alkawarin cewa tunda ba ya garin abin ya faru, idan ya bincika zai yi bayani.

Share.

game da Author