Dalilai 6 da yasa za mu shiga yajin aiki a jihar Zamfara – Kungiyar Kwadugo

0

Kungiyar Kwadugo NLC reshen jihar Zamfara ta bada wa’adin kwanaki 21 ga gwamnatin jihar ta biya ma’aikatan jihar wasu hakkokinsu ko ta shiga yaji aiki.

Shugaban kungiyar Bashir Marafa ya sanar da hakan bayan kammala taron gaggawa da suka yi tare da kungiyoyin kwadugo ‘TUC’ a Gusau ranar Litini.

Bashir Marafa ya zayyan dalilan da ya sa zasu shiga yajin aikin kamar haka;

1. Rashin maida hankali wajen cika alkawuran da gwamnati ta dauka wa ma’aikatan jihar tun shekaru shida da suka wuce.

2. Wasu ma’aikata har yanzu na karban albashin su kasa da Naira 18,000.

3. Gwamnatin jihar ta ki kara wa ‘yan fansho kudin fansho wanda ya kamata a yi shekaru biyar da suka wuce.

4. Rashin daukan ma’aikata musamman yadda wasu suka yi ritaya ko kuma canza wurin aiki .

5. Rashin biyan albashin ma’aikata 1,400 da ta dauka tun a 2014.

6. Gwamnati ta yi watsi da kungiyar kwadugo musamman game da kudin da ta karba daga gwamnatin tarayya (Bailout Funds).

Daga karshe Bashir Marafa ya ce kungiyoyin kwadigon (NUC da NLC) za su fara yajin aikin idan har gwamantin jihar Zamfara bata yi komai akan bukatun ma’aikatan ba.

Share.

game da Author