Matashin nan da ya kashe yarinya, ya cire sassan jikinta ya gudu da caji ofis

0

Hukumar yan sandan jihar Ribas ta sanar da guduwar wannan matashin da ake tsare dashi a ofishin ta da ake wa zargin yi wa wata yar shekara 8 fyade sannan ya cire wasu sassan jikinta.

Da yake tattaunawa da PREMIUM TIMES da ga garin Fatakol, Kakakin yan sandan jihar Omoni Nnamdi ya ce tuni sun fantsama neman sa.

Bayan haka yace jami’in dake kula da kurkukun da aka ajiye shin a da tambayoyi da zai amsa wanda idan har aka gano da hannunsa a ciki lallai zai fuskanci kuliya.

Da yake hira da gidan jaridar Punch, Mahaifin yarinyar Ernest Nmezuwuba yace bayan sun isa ofishin CID sai suka taras babu wutan lantarki. Jami’an da suke tare Johnbosco ya ce ya rubuta bayanan sa, bayan yayi hakan sai ya cirewa yaron ankwan dake hannunsa wai shima ya rubuta nasa bayanan. Daga nan ne fa sai ya bani kudi wai in je in siyo masa ruwa. Ni kuma nace b azan je ba saboda banga dalilin da yasa wai zan siyo wa wanda ya kashe min ‘ya ruwa ba.

Da ya matsa mini ne na tafi, kafin in dawo sai naji wai ai ya gudu daga ofishin.

Ana zargin Ifeanyi Dike dan shekaru 23 wanda yake mataki na Uku a jami’ar jihar Ribas da sace Chikamso Victory a ranar Juma’a da ta gabata.

Kakakin ‘Yan sanda Omoni Nnamdi ya ce wanda ake zargin yayi mata fyade ne daga nan kuma ya kashe ta, ya yanke mata al’aurarta, idanu, harshe, nonuwa ya saka a cikin jakar leda.

Share.

game da Author