Gwamnatin Saudiyya ta ziyyarci ‘yan Najeriyan da aka ci wa mutunci

0

Gwamnatin kasar Saudiyya ta ziyyarci mahajjata daga Najeriya da wasu ma’aikatan kwastom suka ci wa mutunci a filin jiragen saman Yarima Muhammad Bn Abdulaziz a Madinah.

Mataimakin gwamnan Madinah Wahid Asahin ya kai wannan ziyarar ne don bada hakuri kan abin da ya faru da Audu Muhammad da Ibrahim Godi.

Ya kuma tabbatar wa Najeriya cewa hakan bazai sake faruwa ba .

Sakataren hukumar NAHCON Bello Tambuwal ya ce ma’aikatan kwastam sun ci mutuncin ‘yan Najeriyan ne bayan da aka gama binciken takardun tafiyarsu sannan ma’aikatan suka ce su biyosu su kuma suka ki.

Bello Tambuwal yace ya dauki mahajjatan zuwa asibitoci biyu; daya wanda gwamnatin Najeriya ta bude da daya na Saudi sannan gwamnatin Saudin ta amince ta biya duk kudin asibitin su.

Share.

game da Author