An kama wani matashi da ya kai mahaifinsa, kanninsa da abokansa biyar wajen boka don ayi masa tsafi ya yi kudi

0

Rundunar ‘yan sandar jihar Anambra ta kama wani matashi mai suna Chukwuemeka Okafor dan shekara 26 da laifin amfani da mahaifinsa,kanninsa biyu da abokansa biyar wajen yin tsafi domin ya sami samun kudi.

Kwamishanan ‘yan sanda Garba Umar ya sanar da hakan wa manema labarai ranar Alhamis.

Ya ce sun sami kama Chukwuemeka Okafor ne bayan karan aiyukkansa da wani makwabcinsa ya kai ofishin ‘yan sandan.
Garba Umar ya ce Chukwuemeka Okafor ya amince da laifin da ya aikata bayan ‘yan sanda sun gudanar da bincike a kansa.

Ya ce ya yi wa mahaifinsa karya cewa wai zai fara sana’a ne da zata amfanen su amma yana bukatan jarin Naira 100,000. Bayan ya karba ya kai wa bokan hade da hotunan kanninsa biyu da abokansa biyar da ya samu dag shafunansu na sada da zumunta Facebook a yanar gizo.

“Chukwuemeka Okafor ya ce ya fada cikin wannan halin ne bayan wani abokinsa ya yi masa karyan cewa zai kaishi kasar Dubai sannan ya waske masa da kudi da ya kai Naira 400,000.”

‘’ya ce wani abokinsa ne ya fada masa sirrin yadda ya sami kudinsa sannan kuma ya jaddada masa cewa duk ranan da ya fada ma wani wannan sirrin ranar zai mutu.”

Share.

game da Author