An kori dan sandan da ya yi sakaci wanda ya yi kisa da fyaden yarinya ya gudu

0

Rundunar ‘yan sanda ta kori dan sandan da ya yi sakaci har wanda ya kashe yarinya kuma ya cire wasu sassan jikin ta ya gudu a hannun sa. Wanda ya tsere din dai sai da ya fara yi wa yarin mai shekara takwas fyade kafin ya kashe ta.

Tuni aka gurfanar da jami’in dan sandan Johnbosco Okoroeze a cikin ankwa, a gaban Mai Shari’a Sokari Andrew-Jaja da ke kotun Majistare a Fatakwal. An kuma zarge shi ne da laifin hada baki da mai laifi har ya bari ya gudu. Mutane sun bayyana cewa Johnbosco, wanda saje ne na ‘yan sanda, an ga ya na kuka a cikin kotu.

Alkali bai yi wata-wata ba, sai ya ce a kai shi a ci gaba da tsare shi a kurkuku, har sai ranar 14 Ga Satumba, 2017, sannan za a koma da shi kotu, a ci gaba da shari’a.

Johnbosco dai shi ne jami’in dan sanda mai binciken Ifeanyi Dike, wanda ya kashe yarinya Chikamso mai shekara takwas da haihuwa, bayan ya yi mata fyade, daga baya kuma ya cire wasu sassa na jikin ta da su ka hada da al’aura, yatsun hannu, nonuwa da kuma harshe.

Wanda ake zargin dai matashi da ke cikin shekarar karatu ta biyu a Jami’ar Fatakwal.

Wannan tserewa da yayi ta haifar da tashin-tashina a Fatakwal, bayan an rigaya an yayata kama shi da farko da aka yi.

Yayin da iyayen wacce aka kashe su ka zargi ‘yan sanda da hannu wajen barin Ifeanyi ya tsere, su kuma rundunar ‘yan sanda sun ce za su tabbatar da cewa a duk inda ya ke sai sun kamo shi.

Share.

game da Author