Yau Juma’a ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da shugabannin jam’iyyun kasarnan a dakin taro dake fadar shugaban kasa.
Bayanai da suka fito daga wajen taron ya nuna cewa Buhari ya kira shugabannin jam’iyyun ne don su tattauna kan matsalolin da kasa ke ciki musammam wadanda ya shafi yadda ake fiddo magana gangarangan wanda ka iya tada zaune tsaye ko kuma raba hadin kan kasar daga sassan Najeriya.
Shugaban jam’iyyar APC, John Oyegun, Olorunnimbe Mamora, Tony Momoh, tsohon shugaban majalisar dattawa sanata Ken Nnamani da sauransu ne suka jagoranci tawagar jam’iyyar APC in da shugaban rikon kwarya na jam’iyyar PDP, Ahmed Makarfi ya jagoranci tawagar jam’iyyarsa.