Hukumar kula da kiwon lafiya ta duniya WHO ta ce za a iya kawar da cutar Hepatitis idan aka rage yin allurai ga marasa lafiya a asibitoci.
Ta ce yin allura da ake yi a asibitoci musamman wadanda ake amfani da su sau biyu na yada cututtuka kamar kanjamau, Hepatitis da sauransu.
Hukumar WHO ta fadi haka ne a taron wayar da kan mutane kan illolin da ke tattare da yin allura ranar jajibarin taron cutar Hepatitis wanda ake yi ranar 28 ga watan Yuli na kowace shekara.
Jami’ar hukumar WHO Lisa Hedman ta ce alluran da ake iya amfani da shi sau biyu da wasu ababen da ake amfani da su wajen kara jini na da matukar illa domin bincike ya nuna cewa yawan amfani da su ne ya ke kawo cutar Hepatitis C wanda a yanzu yake neman ya zama ruwan dare ga kuma wahalar kawar wa.
Daga karshe Lisa Hedman ta shawarci mutane cewa idan ba ya zama dole bane shan kwayoyi ya fi maimakon allurar domin guje wa kamuwa da cutar Hepatitis da sauran cututtuka.