Idan an Bugi Jaki sai a Bugi Tanki, Daga Comr. Shamsuddeen Chikaji

0

Hakika dukkan zuciya tana son mai kautata mata, kuma haka tana kin duk wanda yace zai munana mata a kowane yanayi, hakan yasa ban fiye ganin laifin duk wani mai kare miradin mai gidansa ba.

Amma sai dai inda gizo yake sakar shine dogaro akan karya tamkar wanda ya dogara da kumfane ta zama tsubirin tsira agare shi yayin ambaliyar ruwa.

Haka yasa nake ganin kamar duk wani toroko da balokoko da yaran Nasir Ahmed El-Rufai sukeyi bai rasa nasaba da lagwadar romo da suke hange wasunsu suke lasawa shi yasa suke danne duk wani halin kunci da damuwa da mutanan jahar kaduna suke ciki, kuma suke nuna kowa na cikin walwala a wannan mulki.

Haka kuma basa bukatar a fadi laifin Mallam Nasir El-Rufai koda kuwa akan menene, mafi yawancin su sun maida shi tamkar wani wanda baya kuskure komai akan daidai yake duk da suna ganin yadda yake wahalar da al’ummar jahar tawajen gazawar sa na biyan bukatu da sauke alkawarurrukan da ya sankamo yayin takarar sa

Mu kuma insha Allah baza mu gaza wajen wayarwa da mutane kai ba da tono dukkan wata tabargaza da badakalar cakwakiya da ake tafkawa a wannan mulki ba, kuma ina kira da ku yaransa da ku daure ku dunga fada masa gaskiya koda kuwa baza tayi masa dadi ba.

Allah ya kara mana ikon fadar gaskiya a duk inda take ya bamu ikon kaucewa karya a duk inda take…Ameeen

Daga: Comr. Shamsuddeen M. Usman Chikaji

Share.

game da Author