Akalla mutane 8 ne suka rasa rayukansu, inda wasu 15 suka jikkita a harin da wasu mata yan kunar bakin wake suka kai a garin Dikwa.
Garin Dikwa dai yana kilomita 80 ne daga cikin garin Maiduguri.
Jiya Juma’a ne wasu mata dauke da bamabamai suka shiga rukunin gidajen gwamnati dake karamar hukumar kuma inda suka tada da bam din.
Wannan hari ya faru ne a daidai kasa na juyayin harin kwantar baunar da Boko Haram suka yi akan wasu Injiniyayoyi da wasu malaman jami’ar Maiduguri dake nemo danyen mai a yankin tekun Chadi da sojojin da ke kare su da yayi sanadiyyar mutuwarsu duka.