Shehu Sani ya fice daga taron bude sabon ofishin EFCC a Kaduna dalilin halartar El-Rufai

0

Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya Shehu Sani ya fice da ga taron bude sabon ofishin EFCC a Kaduna da akayi yau.

Duk da cewa an roke shi da kada ya tafi Sanatan ya ce ba zai iya zama a wajen taron ba ganin cewa wadansu da suka halarci taron na dauke da guntun kashi a duwawunsu da bai kamata ace wai irin wannan taron ne za su halarta.

Hukumar EFCC ta gaiyaci sanata Shehu Sani wajen bude sabon ofishinta a Kaduna. Shima gwamnan jihar Nasir El-Rufai ya halarci taron.

“ Ban ga ta inda hukumar EFCC za ta iya gudanar da wani bancike a Kaduna ba idan dai irin wadannan mutane ne za su halarci bude sabon ofishin nata a Kaduna.

Cikin wadanda suka halarci taron sun hada da wakolin Sarkin Zazzau, Sanata Sule Usman Hunkuyi, tsohon gwamnan jihar Kaduna Ramalan Yero da dai sauransu.

Share.

game da Author