Mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya ce shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu ne zai ci gaba da zama a kujerar shugabancin hukumar daga nan har karshen wannan gwamnati domin ba a shirya canza shi ba.
Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai da ya karanta sakon mukaddashin shugaban kasa Osinbajo a taron bude sabon ofishin hukumar a Kaduna ya ce mukaddashin shugaban kasar ya ce Buhari ya amince da yadda Ibrahim Magu yake gudanar da ayyukar hukumar sannan kuma kowa ya sani cewa shi dinne dai zai ci gaba da rike hukumar.
“ Saboda haka kowa ya sani cewa wannan shine matsayin shugaban kasa. Duk wanda ya ke ganin ba haka ba sai ya yayi kokarin daidaita sahu domin Magu na nan har wata kila shekaru 6 masu zuwa.”
El-Rufai ya ce gwamnatin jihar Kaduna za ta ba hukumar kowani irin goyon baya da take bukata domin samun nasara a aikinta.