Rikicin Fadar Shugaban Kasa da Majalisa: Kowa don aljihun sa ya ke yi

0

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna a zamanin Jamhuriya ta Buyu, Balarabe Musa, ya bayyana cewa wutar rikicin da ke ruruwa tsakanin Fadar Shugaban Kasa da Majalisar Tarayya, ba don kishin kasa su ke yi ba, kowa kishin aljihun sa da muradin sa kawai ya ke yi.

Ya ce matsawar ba a sake tsarin tafiyar da mulkin kasar nan ba, ta za a ci gaba da tafiya mai nisan zango shugabanni na lunke talakawa baibai.

Sai dai kuma ya na da yakinin cewa za a iya samun canji zai iya samuwa matsawar shugaban kasa zai iya daurewa ya yi amfani da wasu kudirori da karfin ikon dokar kasa ta ba shi.

Ya shaida wa kamfanin dillancin labarai a Kaduna cewa tilas sai shugaban kasa ya yi amfani da wadannan dokokin dokin ya samu turba da tubalin zama daram-dakam wajen jawo dukkan ‘yan Nijreiya a jika ta yadda kowa zai san gwamnati na damawa da shi.

“Ka ga dai na farko, Shugaban Kasa ya yi amfani da dokar 1999 ta yadda zai saisaita matsaloli yadda kowa zai yarda kuma ya gamsu da kasancewar Najeriya kasa daya ce, kuma al’umma daya ce.’

“Na biyu, a sauya tsarin da mu ke a kai wanda tsari ne na kishin kai kafin kishin kasa, mu koma kishin kasa shi ne sama da komai.

“Shugaban Kasa ya canja alkiblar tattalin arziki, ya bayar da dama ga jihohi su ja ragamar inganta tattalin arzikin kasa kamar irin yadda tsarin ya ke cikin shkarun 1970 ko ma can baya kafin juyin mulkin 1966.

“Amma ai ganganci ne a ce ana saida kadarorin jihar ko ana saida masana’antunta. Babu kasar da za ta iya ci gaba idan haka kawai da rana tsaka ta ta’allaka tattalin arzikin ta kacokan a kan masana’antu masu zaman kansu.” Inji shugaban jam’iyyar PRP.

Share.

game da Author