Sarkin Musulmi Abubakar Saad ya yi kira ga matasa da ‘yan mata da su daina mai da hankulansu ga shafunanar sada zumunta a yanar gizo kamarsu instagram, 2go, Facebook da dai sauransu fiya da karatun Alkurani da sanin addini.
Dr. Saad ya fadi haka ne a wajen rufe taron gasar karatun Alkurai da akayi a garin Sokoto.
Ya ce yanzu za ka ga matasa sun kashe lokutansu a rana kaf a shafunar sadarwa na yanar gizo mai makon yin wasu abubuwan da zai amfane.
“ Abin tashin hankali kwarai shine ganin yadda mai makon matasa da ‘yan mata su mai da hankulansu ga karatu sai kaga kullum suna shafunan Facesbook, twitter, 2go, Instagram da dai sauransu.
“Yadda yanzu ‘yan mata ke bata lokuttansu a irin wadannan shafuna abin lura ne ga iyaye.”
Ya ce da mata za su fi mai da hankali ga karatun Alkurani da dai sauran a ababen da zai gyara rayuwarsu da yafi mai makon shafunan da suke bata lokuttansu akai a yanar gizo. “ Hakan zai sa su zamo uwaye na gari nan gaba.”
Discussion about this post