Kasar Amurka ta tallafawa karamar hukumar Bwara da Daloli domin kamala ginin cibiyar kiwon lafiya a kauyen Jikoko

0

Cibiyar kula da kiwon lafiyar da ke Jikoko karamar hukumar Bwari a Abuja ta sami tallafin kudi dala 10,000 daga gwamnatin Amurka domin kammala ginin asibitin dake kauyen.

Da yake tofa albarkacin bakinsa a wajen taron dora harsashin ginin cibiyar Jami’in gwamnatin Amurka David Young ya ce ba wannan karo bane kawai kasa Najeriya ke amfana da tallafi daga kasar Amurka domin duk shekara kasar ta kan ba Najeriya tallafin Kudade domin bunkasa fannin kiwon lafiya a kasar da ya kai dala miliyan 7.35 ta hukumar USAID.

Ya kuma kara da cewa Najeriya ta samu Karin tallafi na dala miliyan bakwai da ga hukumar USAID a shekaran bara.

David Young ya ce har yanzu Najeriya na fama da cutar shan inna da wasu cututtuka wanda ya kamata cibiyoyin kiwon lafiya su daura damara wajen kawar da su a kasar domin rage yawan mutuwan musamman mata da yara kanana.

Daga karshe shugaban karamar hukumar Bwari Musa Dikko ya mika godiyarsa ta musamman ga gwamnatin Amurka sannan ya roki kasar da ta fadada wannan tallafi da take ba Najeriya zuwa fannonin Ilimi, yawan bude ido da sauran su domin hakan zai samar da aikin yi wa matasan kasar.

Share.

game da Author