Ku rabu da AbdulAziz Yari fa – sakon Kungiyar Gwamnoni ga hukumar EFCC

0

Kungiyar gwamnonin Arewa ta yi kira ga hukumar EFCC da ta daina muzguna ma shugaban kungiyar gwamnonin kuma gwamnan Zamfara AbdulAziz Yari da ta keyi kan wani rahoton wani gidan jarida wai yana gina wani Otel a garin Legas da yakai dala miliyan 3.

Mai Magana da yawun kungiyar Abdulrazak Barkindo ya ce gwamnonin sun ce hukumar ta rabu da Yari ko ya mai da hankalinsa wajen jagorancin kungiyar da jiharsa.

“ Abdul Aziz yari ya fadi ya kuma ta nanatawa cewa bashi da mallakin fili ko wata Otel da yak e ginawa a jihar.”
Sun yi kira ga hukumar EFCC din da su mai da hankalinsu wajen kamo masu laifi ba wadanda ba su da laifin komai ba.

Share.

game da Author