Uwargidan Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ta shaida wa Babbar Kotun Ikeja da ke Lagos cewa, Fasto Akpan-Jacobs wanda ya damfare naira milyan 918, dan aike ne a wurin ta.
“Ni na biya naira milyan 49 a matsayin filin da za mu gina ofishin THA Shipping, abokin hulda ta Fred Holmes bai bayar da gudummawa wajen sayen filin ba, amma ya bayar a wurin aikin gini.”
“Akpan-Jacobs na damka wa kudin sayen fulotin, amma sai ya kasance ban san ko a wurin wa ya sayi fulotin ba. Don haka bai bayar da ko sisi a matsayin gudummawa ba, shi fa tamkar kawai dan aike ne a wuri na.” Haka Titi ta shaida wa kotu.
Kamfanin Dillancin Labarai ya ruwaito cewa hukumar EFCC ta na cajin Akpan-Jocobs da laifuka har 14 da suka hada da cin amana, hada baki a yi cuta, maida dukiyar wani har ta naira milyan 918 mallakar THA Shipping Maritaime Ltd., a matsayin ta sa.
Wannan kamfani dai Titi da Akpan-Jacobs da kuma Fred Holmes ne suka kafa shi tun cikin 2000, amma a yanzu su ke a kotu domin neman hakkin wanda ke da mallakar kamfanin.
Idan ba a manta ba, watanni biyu da suka gabata, Premium Times Hausa ta kawo cikakken labarin wannan harkalla da kuma yadda aka fara zama a kotu.