Babban hafsan rundunar sojin Najeriya, Janar Tukur Burutai ya umurci shugaban dakarun sojin Lafiya Dole Janar Attahiru da ke aikin samar da zaman lafiya a dazukar jihar Barno da yaki da Boko Haram cewa ya basu kwanaki 40 su kamo shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau.
Buratai ya fadi haka ne a wata sako da ya fitar wanda kakakin rundunar soji Janar Sani Usman ya saka wa hannu.
Buratai ya ce Janar Attahiru ya yi amfani da duk wani dabara da makaman da zai bukata domin ganin dakarun sojin sun kamo Shekau a duk inda yake nan da kwanaki 40.