Gwamnatin kasar Japan ta bada tallafi don gyarar cibiyar kiwon lafiya da ke kauyen Shere karamar hukumar Bwari, Abuja.
Jakadar kasan a Najeriya Sadanobu Kusaoke ya ce sun yi haka ne don taimaka wa wajen ganin an bunkasa aiyukkan kiwon lafiyar mutanen yankin musamman ganin cewa sibitin na fama da matsaloli kamar su rashin ma’aikata, rashin ingantattun kayayyakin aiki da sauran su.
Cikin aiyukkan gyaran da gwamnatin Japan din ta yi ya hada da samar da sabin gadaje 15, kayayyakin aiki, na’urorin samar da wutan lantarkin da hasken rana da sauransu.