Dalilin da ya sa magani cutar Kanjamau baya ma wasu aiki – WHO

0

Hukumar kula da kiwon lafiya ta duniya WHO ta ce zata samar da hanyoyi don kawo karshe yadda wasu magungunar cutar kanjamau baya ma wasu aiki a jikinsu.

Shugaban hukumar WHO Tedros Ghebreyesus ya sanar da haka a taron da hukumar ta shirya kan bada rahotanni kan matsalolin da ake fama da su na rashin aiki da maganin cutar kanjamau ya ke yi wa wasu masu dauke da cutar.

Ya ce rashin kiyaye yadda ya kamata a sha maganin na haddasa irin haka.

Daga karshe wani jami’in hukumar WHO Gottfried Hirnschall ya shawarci kasashen da ke fama da irin wannan matsalar da su yi amfani da salon shirin kawar da wannan matsalar da hukumar WHO ta samar domin rage yaduwar cutar sannan kuma da ceto rayukan mutanen kasashen su.

Share.

game da Author