Jam’iyyar APC ta bayyana cewa Shugaban Kasa Muhammadu ya na murmurewa a cikin sauri, sabanin jita-jitar da ake yi cewa ya na cikin halin mutu-kwakwai-rai-kwakwai.
Shugaban jam’iyyar, John Odigie-Oyegun ne ya bayyana haka a Abuja, a yayin da ya ke jawabi ga manema labarai bayan kammala taron kwamitin gudanarwar jam’iyyar na kasa tare da gwamnonin jam’iyyar APC.
“Mu na farin cikin shaida maku cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya na samun sauki kwarai, kuma ya na kara samun kuzari.
” Mu na fatan ya ci gaba da bin kadin jiyyar da ya ke yi a hankali, kuma idan ya dawo,mu na da yakinin kara daukar aniyar ayyukan da ke gaban sa ka-in-da-na’in.
Sai dai kuma ya bayyana cewa likitan Buhari ne kadai zai iya bayyana ranar da shugaban zai dawo Najeriya.
Oyegun ya ce ba zai maida Wa gwamna Fayose na jihar Ekiti amsa ba, sai idan haka ta taso nan gaba.
Kwanan baya ne dai Fayose ya ce Buhari na can a asibiti mutu-kwakwai-rai-kwakwai, shi kuwa Oyegun ya ce maida hankali kan Fayose soki-burutsun da ya ke yi kamar daukar sa ne da muhimmanci. Dalili kenan ya ce ba zai kaskantar da kan sa ya biye wa Fayose su na ka-ce-na-ce a shafukan jaridu ba.