Abubuwa 3 da ke hana mace daukar ciki

0

Wata babbar likita Ifeoma Amugu ta ba da wasu dalilai da ta ce suna daga cikin manyan abubuwan da ke hana mata daukan ciki wanda yakan zama ko daga wurin ta ne ko daga mijinta.

1 – Yadda mutum zai iya zuwa kowani shagon magani ya siya maganin da ya ke so ba tare da ya nuna wata shaidar bukatar haka ba daga wani kwararren likita.

Ifeoma ta ce hakan na sa mutane a dirka magunguna a cikin su wanda daga baya yakan zama sanadiyyar lalacewar mahaifansu ba su sani ba.

Sai kaga an yi aure amma ciki ya ki shiga ko kuma zama.

2 – Rashin kwanciyar Hankali na sa mace ta kasa daukar ciki.

3 – Matsanancin shan giya da taba sigari ga mace ko namiji na hana daukar ciki.

Daga karshe likita Ifeoma ta shawarci iyaye da su kula da tarbiyar ya’yan su sannan ta yi kira ga iyaye da su ba ya’yansu tazara wajen haihuwa.

Share.

game da Author