An bayyana cewa dakarun sa-kai na sintiri, wato Civilian JTF, sun yi asarar jami’ai har 680 daga shekarar 2012 zuwa yanzu. Lauyan JTF din ne mai suna Junril Gunda ya ya bayyana haka a wata hira da kamfanin dillancin labarai, NAN.
Gunda ya jaddada cewa duk da yin duba da irin dimbin asarar rayuka da suka yi, hakan zai sare musu guiwa wajen kara zage damtse su kare rayuka da dukiyoyin al’umma daga Boko Haram ba.
“Wannan kungiya ba ta neman riba ba ce, an kafa ta ne cikin 2012, a lokacin da matasan mu suka yanke shawarar daukar sanduna da kulake su na fatattakar Boko Haram daga cikin birnin Maiduguri.
” Saboda ba mu da wani gida sai fa Barno, shi ya sa mu ke aiki bakin rai bakin fama domin mu tabbata da kare Maiduguri daga duk wata barazanar Boko Haram.
“Abin takaici sai asarar rakuyan yaran mu matasa mu ke yi. A kullum sai ka ji labarin an kashe dan sa-kai na JTF, amma hakan ba ya na nufin za mu daina kare kasar mu daga ‘yan ta’adda ba.
” Kun ga dai ni din nan lauya ne cikakke har ofis na ke da shi, amma kuma ina aikin sintiri na sa-kai din JTF, kuma har horo sojoji sun yi min na tsawon watanni takwas.
“Idan na ga dan Boko Haram yanzu, zan iya sa bindiga na bindige shi kawai.
Ya yi kira ga gwamnati da ta rika daukar dawainiyar ‘ya’yan su, da kuma iyalan wadanda suka rasa rayukan su a bakin dagar yaki da Boko Haram.
Ya ce sama da matasa dubu 23,000 aka dauka aikin sa-kai a dukkan fadin jihar Barno.
A na su bangaren, ya ce gwamnatin jihar Barno ta na biyan su naira 15,000 a wata. Ya ce mambobin su sun kai 1400.