Maitaimaka wa shugaban kasa a kan harkar yada labarai Garba Shehu ya sanar da cewa shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya umurci maraimakinsa da ya rattaba hannu a kasafin kudin 2017.
Garba Shehu ya sanar da haka ne a wata sanarwa da ya saka wa hannu daga fadar shugaban kasa.
Yanzu dai an kammala shiri tsaf domin hakan.
Ko da yake Osinbajo na jihar Anambra yanzu haka, ana sa ran zai dawo da yamman yau domin saka hannun.
Shugaban majalisar dattijai Bukola Saraki da na Wakilai Yakubu Dogaro duk sun iso Aso Rock.