Babban jagoran mabiya darikar Katolika na duniya da ke Birnin Rome, Fafaroma Francis, ya bai wa wasu limaman darikar Katolika ‘yan Nijeriya wa’adin yin biyayya ga hukuncin sa, ko kuma su rasa aikin su.
Wani rahoto da kamfanin dillancin labarai na Associated Press, AP ya ruwaito, ya nuna cewa Fafaroman ya yi wani zama da tawagar limaman a fadar Vatican, da suka je daga Ahiara, da ke kudu maso gabacin Nijeirya, wadanda suka ki amincewa da nadin jagoran su, wani Bishop da tsohon Fafaroma Benedict ya yi tun cikin 2012.
Jaridar fadar Vatican mai suna L’Osservatore Romano, ta ce Fafaroman ya yi wannan kakkausan gargadi wanda ba a san shi da nuna irin wannan fushi ba, inda ya yi barazanar dakatar da su idan ba su bi umarnin da aka ba su ba, cewa tlas su amince da nadin Bishop Peter Okpaleke a matsayin shugaban su.
‘’Duk wani limamin da ya ki amincewa da Bishop Peter, to ya na kokarin tarwatsa kan wannan darika ta Katolika ce a can Nijeriya, kuma ni ma ina fushi da shi.’’ Haka Fafaroma ya shaida musu a fusace.
Cocin mabiya darikar Katolika dai ya na da dimbin mabiya a Afrika da kuma Amurka ta Arewa.