Basaraken Auchi, Otaru Aliru Momah da ke jihar Edo, ya bayyana cewa sojoji sun kama ‘yan Boko Haram 24 a cikin yankin sa.
Basaraken ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da ya yi da kamfanin dillancin labarai, NAN, a fadar sa ta Auchi, cikin karamar hukumar Etsako-ta Yamma a ranar Litinin.
Ya ce Kwamandan Sojojin Makarantar koyon aikin injiniya da ke kusa da Auchi ne ya bayyana masa kama wadanda ake zargin da ya kai masa ziyara a fadar sa. Ya ce wa kamfanin dillancin labarai Kwamandan bai ma dade da barin fadar tasa ba kafin wakilin kamfanin ya isa.
Ya bayyana min cewa ‘yan Boko Haram din su na yin shigar-burtu ne su saje da makiyaya, a matsayin su ma Fulani makiyayan ne.
Otaru na Auchi ya ce tuni an kwashi wadanda ake zargin an tafi da su Benin, hedikwatar jihar Edo. Daga nan sai ya jinjina wa Kwamandan makaranatar sojojin dangane da saurin kai daukin da suka yi, tun kafin a kai ga yin wani mummunan hari a yankin, inda ya ce shi dama sha’ani na tsaro abu ne mai bukatar kyakkyawan shiri da kuma saurin aiwatarwa.
Bayan nan kuma basaraken ya bayyana cewa su na fama da matsalar Fulani makiyaya a yankin na sa, har ma ta kai mun sanar da manoman su musamman mata su daina zuwa gona kawai har sai abin da Allah ya yi.
‘’Yanzu haka ma mun dan ba kowace mace jari, mun ce ta yi sana’a, ta daina zuwa gona, kafin komai ya lafa.”