‘Yan gudun Hijira: Yan Najeriya sama da 270 ne zasu dawo daga kasar Kamaru

0

‘Yan Najeriya sama da 270 ne zasu dawo kasa bayan tilasta musu da Kasar Kamaru ta yi da su bar sansanonin da ke kasar su dawo Najeriya.

Hukumar NEMA tace za ta karbe su a garin Yola, jihar Adamawa.

Duk da cewa kasar Najeriya bata ji dadin abinda kasar Kamaru tayi kan ‘yan gudun hijiran da suke kasar ta ba na tilasta musu da su dawo, ta ce hakan ya saba ma yarjejeniyar dake tsakanin kasa da kasa na majiaisar dinkin duniya musamman wanda ya shafi ‘yan gudun hijira.

Gwamnatin jihar Barno da hukumar dake kula da al’amuran ‘yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya sun nuna bacin ransu akan hakan.

Babban jami’I a hukumar Hafeez Mohammed Bello yace ‘’yan gudun hijiran za su shigo Najeriya ta bodar Sahuda sannan kuma a karbe su a sansanin dake Burn Bricks a karamar hukumar Mubi dake jihar Adamawa.

Ya ce cikin ‘yan gudun hijiran da za su karba akwai tsofafi, mata da kananan yara.

Share.

game da Author