Wani abin al’ajibi ya faru a jami’ar Maduguri inda aka tsinci jariri a ban dakin kwanan matan jami’ar.
Wasu daga cikin daliban jami’ar sun sanar wa gidan jaridar PREMIUM TIMES cewa an tsinci jaririn ne bayan anji kukan sa a cikin bayin daidai wasu dalibai mata suna kokarin komawa daki.
Bayan da wadanan mata suka ga jaririn sai suka kira ma’aikaciyar da ke kula da dakin kwanan nasu wato ‘Matron’ da mai gadin dakunan matan.
Da ma’aikaciyar ta zo sai ta ciro jaririn daga cikin ramin bayin dauke da raunuka a fuskarsa.
Daya daga cikin daliban da suka tsinci jaririn ta ce “Da aka haifi jaririn sai uwar ta yi kokarin tura shi cikin ramin bayin amma saboda girman jikinsa ya kasa wucewa.”
“Wannan shine ainihin muguntar da bata da na biyu nan taba gani a tsawon rayuwata.”
Da muka nemi ji ta bakin hukumar jami’ar, Ahmed Muhammed ya ce hukumar makarantar za ta bi diddigin wannan al’amari kuma domin hakan yana neman ya zamo ruwan dare a jami’ar.