Gwamnoni jihohi 36 sun tsaya a kan cewa a sake kulla wata sabuwar yarjejeniya da kamfanonin jiragen da za su yi jigilar mahajjatan bana.
A shekarar da ta gabatac dai kamfanoni biyu ne kacal daga Najeriya, wato Max Air da kuma Medview, sai kuma wani kamfanin kasar Saudi Arabia mai suna Fly Nas aka ba aikin jigilar mahajjatan.
Shigo da kamfanin Fly Nas ya haifar da cece-ku-ce, inda har wasu da dama da ke da ruwa da tsaki a harkar suka rika gunaguni da korafin dalilin shigo da Fly Nas a harkar jigilar, maimakon wasu kamfanonin cikin gida Najeriya.
Sai dai kuma, Hukumar Kula da Aikin Hajji, NAHCON, ta bayyana wa Premium Times cewa, ba ta da wani hurumin shiga harkar jiragen da za su yi jigila sosai, domin hukumar ta na bin sharudda ne da kasar Saudi ta gindaya cewa kowacekasa dai sai ta ba jirgin kasar Saudi damar daukar mahajjatan ta.
Biyo bayan wannan koke-koke ne ya sa shugaban hukumar kula da Alhazai, Abdulllahi Mohammed ya halarci wani taro da gwamnonin, inda ya yi masu cikakken bayani, a dakin taro na fadar Shugaban kasa, a ranar Laraba.
Tsohuwar yarjejeniyar dai wadda aka sa wa hannu tun a cikin watan Fabrairu, 2015, ta amince da cewa Najeriya za ta bada hidimar jigilar kashi 25 cikin 100 na mahajjatan da za su tashi a karkashin gwamnati, a 2016 kashi 35 bisa 100, sai kuma kashi 45 bisa 100 a 2017, da kuma 50 bisa 100 cikin 2018 mai zuwa, duk ga kasar Saudiyya din.
Wata takarda da gwamnan jihar Zamfara Abdul’azeez Yari ya sa wa hannu, a madadin sauran gwamnonin, ta bayyana cewa, za su yi iyakar na su kokari, domin ganin cewa kamfanonin gida Nijeriya sun amfana da wannan aikin jigilar.
Har ila yau, gwamnonin sun karbi rahoto dangane da rufe kan iyakokin kasar nan, daga hannun shugaban hukumar kwastan, Hamid Ali, wanda mataimakin shugaba na riko, Dangaladima Alhaji ya wakilta. Sun kuma karbi wani rahoton daga dataktan Babban Bankin Duniya da ke Najeriya, Rachid Ben Messauod dangane da wata yarjejeniya da tsakanin bankin da jihohi.
Rahoton hukumar kwastan dai na runshe ne da bayanan kara sa ido wajen karfafa hana fasa-kwauri da hukumar ke yi, kuma gwamnonin su ka sha alwashin kara hadin kai da hukumar ta hana fasa-kwauri domin tabbatar da cewa kasar nan ta kai gacin samar wa kan ta yawan shinkafar da za ta wadaci kasar baki daya nan da shekarar 2018.