Kotu a Okene jihar Kogi ta yanke wa wasu barayin shanu, Muhammed Lawal Jauro da Yusuf Sani hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Alkalin kotun Josiah Majebi ya yanke hukuncin ne bisa ga laifin da suka aikata na satan shanun wani Haruna da kuma kisan da suka yi mishi.
Wanda ya shigar da karan Dauda Abdullahi ya ce ya kai karan su ne a watan Janairu 2016 kan kisa da kuma sace shanun wani abokinsa Haruna da suka yi a dajin Okene.
Ya ce ‘yan sanda sun kama su ne a Ajase-Ipo jihar Kwara amma kuma shi shugaban su Awaijo Wetti ya gudu.
Alkalin Majebi ya yanke wa kowanen su hukuncin zama a kurkuku na tsawon shekaru 28 sannan kuma kisa ta rataya saboda aikata kisan da suka yi wa Haruna .