AMSOSHIN TAMBAYOYI tare da Imam Muhammad Bello Mai-Iyali

1

TAMBAYA: Menene matsayin Masturbation a Musulunci, wato mutum yayi ta taba gabansa har sai maniyi ya fito masa? Wasu na cewa wai za a iya haka idan mutum ya matsu. Shin menene musulunci ya ce akai.

AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad SAW.

Masturbation: shi ne Wasa da Al’aura, wanda a larabce aka sansa da “Istimna’i”. Wannan yana nufin yin amfani da hannu, yatsa ko wani abu domin biyan bukatar jima’i ga mutum da kansa da tunanin saduwa da wata mace ko wani namiji, ga mace. Wasa da Al’aura ga maza, sukan yi amfani da Sabulu ko Mai ko wani abu mai yauki da santsi ta hanyar mulmula Azzakarinsu har su biya bukatar su. Amma mata, suna amfani da yatsa ko kyandir ko wani abunda za su tura cikin gabansu, har su biya bukatar su.

Ya ‘yan uwa, wannan matsala ta Wasa da Al’aura, dabi’a ce abin kyama saboda wasu dalilai, wato dalilan addini, na al’ada, da kuma na lafiya.

Malaman Musulunce sun tafi akan HARAMCIN Wasa da Al’aura don biyan bukata, dalilin fadan Allah (SWT): ‘Da wadanda suke, gafarjojinsu, masu tsarewa ne. Sai fa akan matansu… To, duk wanda ya nemi abinda yake a bayan wannan, to, wadannan su ne masu ketare iyaka’ (Mara’rij 29 – 31, Muminun 2- 4), ‘ Kuma wadannan da ba su samu aure ba, sukame
kansu har Allah ya wadatar da su daga falalarsa… (Annur 33)
{وَلْيَسْتَعْفِفْ الَّذِينَ لا يَجِدُونَ نِكَاحاً حَتَّى يُغْنِيَهُمْ
اللَّهُ مِنْ فَضْلِهِ} (النور 33)، {والذين هم لفروجهم حافظون * إلا على
أزواجهم أو ما ملكت أيمانهم فإنهم غير ملومين * فمن ابتغى وراء ذلك
فأولئك هم العادونْ} (المعارج 29 – 33)

Hahamcin wannan dabi’a ta Wasa da Al’aura, fahimta ce ta manyan malaman duniya, kamar Malikiyya, Shafi’iyya, Hambaliyya, Shi’a, Ibn Taimiyya, Ibn Kayyim, Ibn Baz, Usaimin…

Dukkan Musulmi an umurce shi da ya yi aure, in ba zai iya ba, yayi Azumi, Kuma ya tsare idonsa da kunninsa da ga kallo ko sauraren batsa da al-fasha. Musulunci ya yi umurni da haka ne tare da karanta cin abinci don rage sha’awa.

Lokacin da bawa ya bi dukkanin hanyoyin da muka ambata don tsare kansa da ga zina, amma ya kasa samun saukin sha’awar sa, to, Malamai suna ganin idan yayi Wasa da Al’aurar sa don gudun fadawa ga halakar Zina, to, ba bu laifi akan sa, sabo da lalura.

Duk da yake dai malamai sunyi sauki akan mas’alar Wasa da Al’aura (istimna’i) don biyan bukata, sa bo da lalurar tsananin sha’awa.

Binciken masanan kimiyyar lafiya ya nuna cewa YAWAN WASA DA AL’AURA (excessive masturbation) nada illa ga lafiya. Kuma ya zama matsala ga magidanta, don wasu har bayan aure ma suna yi, don ba su samun gamsuwa, sai sun yi abinan da suka saba da shi, wato, Wasa da Al’aura (istimna’i).

A shari’ance kuwa, shari’a za ta hukunta duk wanda aka sa me shi da wannan laifi. Kuma shari’a ta wajabta tuba a gareshi. Allah ya tsare bayin sa da ga dukkan mummunar dabi’a. Amin.

Allah she ne mafi sani.

TAMBAYA: Matan da ta sha azumi saboda ciki da take dashi. Bayan ta haihu kuma shayarwa da ciwon Ulcer da take da shi ya hana ta biyan wadannan azumi da ta sha har wani azumin yazo. Shin za ta iya ciyarwa kawai shikenan ko kuma dole sai ta rama azumin bayan wannan?

AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad SAW.

Mai cikin da ta sha Azumi, Hukuncinta shi ne rama adadin kwanakin da ta sha.

To, amma sai gashi rashin lafiya da shayarwa ya hana ta rama azumin.

To, hukuncin ta annan shi ne hukuncin mara lafiya.

Idan ana sa ran warkewa da ga ciwon, to sai ta jira, har sai ta warke, sannan ta rama azumin da ta sha. Idan kuwa ba a sa ran warkewan ciwon, kamar ciwon Ulcer, sai ta ciyar da miskini daya a mamadin ko wace ranar da ta sha azumi.

Lallai Allah SWT ya fada a cikin Al-kur’ani cewa: Lallai yin azumi shi ne mafi alkhairi ga duk masu ikon yin azumin.

Allah shi ne mafi sani.

TAMBAYA: Menene hukuncin mace da ke yi wa mijinta karya?

AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad SAW.

Karya dai haramun ne, kuma zunubi da ga cikin manyan zunubbai, makaryace dan wuta ne, hukuncinta ta bar karya kuma ta tuba zuwa ga Allah. Kar ta kuskura ta mutu a matsayin makaryaciya.

Nana Ummu-Kulsum ta ruwaito cewa Annabin tsira S.A.W ya yi rangwame ga ma’aurata su yi karya cikin abinda zai inganta zamantakewar su, na duniya ko lahira. Kamar yadda hakan kuma ya halatta don kyauta ta kauna da soyayya, ko kaucewa fitina a tsakanin su.

To, da wannan hadisi da Imamu Muslim ya ruwaito, kenan ya hallata ga mace ta yima mijinta karya bisa wadannan sharudda:

1. A cikin a binda zai inganda rayuwar auren su, a duniya ko lahira.

2. A cikin a binda ba zai cutar da mijin ba, cikin addini, dukiya, lafiya, duniya ko lahira.

3. A cikin a binda babu yaudara ko zalunci.

4. A cikin a binda ba zai tauye masa hakkin sa ba. Ko kuma ya hana masa hakkin sa.

5. A cikin a binda ba sabawa Allah ba ne da Manzon sa SAW.

Ya ‘yan uwa, Musulunci ya bada mahimmanci kwarai ga lamarin iyali (Family Unit), sa bo da haka ne, ya halatta karya cikin a binda zai ingata iyali (Family Unit), ba tare da cuta ko cutarwaba. Lallai ne ma’aurata su ji tsoron Allah, kar su yi karyar da zata tarwatsa iyali (Family Unit), yin hakan zalunce ne mai girma.

Share.

game da Author