An sako ‘yan matan Chibok 80

0

Kungiyar Boko Haram ta sako ‘yan matan makarantar sakandaren Chibok da tayi garkuwa dasu tun 2014.

Koda yake bamu sami tabbacin ko su nawa bane aka sako, gidan jaridar Saharareporters sun bada rahoton cewa akalla sama da ‘yan mata 80 ne aka sako.

Duk da cewa ya saka a shafin sadar da zumuntarsa na twitter da muka nemi ji da ga bakinsa, Sanata Shehu Sani wanda kuma yana daya daga cikin wadanda suka yi zaman tattaunawar a wancan karon da har yayi sanadiyyar sako ‘yan mata 21 a wancan karon yace tabbas akwai wannan magana sai dai bai san ko nawa aka sako ba.

Share.

game da Author