A kullum dai idan kana raye ba zaka rasa jin wani abu da zai tada maka da hanlaki ba ko kuma ya saka cikin matsanancin tunani ko ko ka dade ka na dariya.
A garin Baure dake Bawa a mazabar Karfi dake karamar hukumar Kura Jihar Kano wasu abokanai kuma makwabta suna ta tafka shari’a a kotu saboda Zabuwa.
Wadannan makwabtan juna Alh Ado da Mal. Shuaibu suna kiwon zabine a yankin nasu. Alh. Ado ya zargi Mal. Shuaibu da sace masa zabuwar sa in da rikicin ya kai su har zuwa ga dakacin yankinsu duk da ya nemi sulhuntasu a wancan lokacin hakan bai yiwu ba dole ya bar su suka gai ga zuwa ofishin ‘Yan sanda inda dai abin ya kai su har zuwa ga sun shiga kotu akai.
Ita dai wannan Zabuwar anyi siyo ta akan naira 1,300.
Shi dai Alhaji Ado ya shaida wa Kotu cewa yana zargin Mal. Shu’aibu ne ya dauke masa Zabuwarsa da take kwai domin a yammacin ranar da ta bace, ya ji kamshin suya a gidan Mal. Shua’abu.
Dantala Kura da yake bibiyar wannan rikici ya sanar damu cewa Mal. Shu’aibu ya musanta hakan inda ya ce ba zabuwar Alh. Ado bane ta shi ce domin ranar ya siyo ta a kasuwa.
Yanzu dai kowa ya dauki lauyar sa domin Kareshi a kotu wanda za ta ci gaba da zama ranar Laraba mai zuwa.