Jami’an tsaro sun dakile harin ‘yan kunar bakin wake a Maiduguri

0

Jami’an yan sandan Jihar Barno sun dakile wata hari da ‘yan kunan bakin wake suka nemi ta da wa a garin Maiduguri.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Damian Chukwu ne ya sanar da hakan wa manema labarai a garin Maiduguri.

‘Yan banga ne suka tare su a garin Mamanti Jajere kafin su shiga garin Maiduguri, inda kafin su yi wani abu an fatattakesu.

“Ana cikin haka ne daya daga cikinsu ta tada bamabamai dake daure a mararta. Nan take ta mutu inda sauran biyun kafin su ce zasu aikata wani abu an harbe su.

Share.

game da Author