Dakarun Sojin Najeriya sun gano boyayyaun makamai a kudancin Kaduna

0

Kakakin rundunar sojin Najeriya Janar Sani Usman ya sanar wa manema labarai cewa dakarun sojin Najeriya sun gano wasu makamai masu yawa da aka boye a kauyukan, Gwaska, Dangoma, Angwan Far da Bakin Kogi dake yankin kudancin Kaduna din.

Sojin ta samu nasaran hakan ne a ci gaba da aikin da ta ke yi a dazukan kudancin Kaduna mai suna ‘Operation Harbin Kunama’.

Makaman da aka gano sun hada da bindigogi dirar hannu, da alburusai da dai sauransu.

Wannan shiri na ‘Operation Harbin Kunama’ ya hada da dazukan da sukayi iyaka da jihohin Bauchi, Kano da jihar Filato.

Share.

game da Author