Ministan yada labarai Lai Mohammed ya sanar wa manema labarai a fadar gwamnati bayan taron majalisar zartarwa da keyi duk mako cewa dalilin da ya sa shugaban kasa Muhammadu Buhari bai sami daman halartar zaman na yau ba shine don yana halartar wasu ayyuka da basu bashi daman halarta ba.
Lai ya karyata rade-radin da ake ta yadawa wai rashin lafiya ne ya sa Buhari bai halarci zaman na yau ba.
Yace ba wani abu sabo bane don mataimakin shugaban kasa ya jagoranci zaman majalisar.