TATTAUNAWA: Ma’aikatan Jinya kwararru ne, sun cancanci zama shugabannin manyan asibitocin kasa

0

Shugaban kungiyar unguwar zoma da ma’aikatan jinya na kasa NANNM Adeniji Abdulrafiu Ajani ya yi hira da gidan jaridar PREMIUM TIMES inda ya ba da bayanai akan matsalolin da bangaren jinya na kiwon lafiya ke fama da su da yadda kungiyar sa ke kokarin ganin gwamnati ta kawo musu dauki akan hakan.

PT: Menene matsayin kungiyar unguwar zoma da na ma’aikatan Jinya na kasa ta keyi akan yajin aikin da ma’aikatan suke yi yanzu haka a jihar?

ADENIJI: Bangaren kiwon lafiya a kasa Najeriya na fama da matsaloli da dama wanda ya hada da nuna halin ko in kula da gwamnati takan yi wa bangaren.

Ma’aikatan jinya na jihar Ondo sun gudanar da yajin aiki saboda rashin biyan su wasu bukatun su da gwamnati ta kasa yi da ya hada da bashi kudaden albashinsu wanda gwamnati har yanzu ta kasa biyansu cikakken abinda ya kamata a biya su.

PT: Me za ka ce akan rashin jituwan da ke tsakanin likitoci da ma’aikatan jinya a asibitoci sannan kuma menene ke kawo rashin jituwan su?

ADENIJI: Rashin jituwan da ke tsakanin likitoci da ma’aikatan Jinya na faruwa ne saboda fifiko da gwamnati take nuna ma likitoci akan ma’aikatan jinyar.

Za a samu maslaha akan irin wannan matsala ne idan har gwamnati ta daraja kowa akan aikinsa, ta daina nuna fifiko ga daya daga cikinsu wajen biya musu bukatu.

PT: Me zaka ce akan bambamci da ke tsakanin likitoci da ma’aikatan jinya duk da cewa suma ma’aikatan jinya na samun horo a fannin aikin a makarantun koyar da unguwar zoma?

ADENIJI: Duk darussan da ake karantar wa idan kana karatun likita ana karantar dasu a makarantun koyar da ma’aikatan jinya sai dai banbancin shine kafin ma’aikacin jinya ya fara aiki bayan ya kammala karatun sa sai ya rubuta jarabawan kwarewa wanda kungiyar ma’aikatan jinya da unguwar zoma ta ke shirya wa. Kuma doka ne a aikin cewa duk wanda bai rubuta wannan jarabawar ba,ba zai iya yin aiki jinya ba sai dai zai iya koyar wa a makarantun koyar da ma’aikatan Jinya.

PT: Menene shawaran ka akan shugabancin manyan asibitoci da ake ba likitoci kawai ?

ADENIJI: Hakan bai dace ba saboda fannin kiwon lafiya ba fanni daya bane. kamata ya yi ace duk wanda zai iya rike kujeran shugabanci a bashi, likita ne ko ma’aikacin jinya.

PT: Menene dalilin da ya sa ma’aikatan jinya ke barin kasa Najeriya zuwa wasu kasashe?

ADENIJI: Ba komai ke kawo hakan ba illa rashin biyan ma’aikatan jinya albashi mai tsoka, rashin kayan aiki, rashin kyakkawar wurin aiki, rashin ma’aikata da kuma sauran su. Amma hakan zai iya canzawa idan gwamnati ta mike tsaye sannan ta maida hankalinta wajen bunkasa fannini da kuma wadata da abinda ake bukata musamman a asibitocin kasar nan.

PT: Menene kungiyar NANNM ke yi don kawo karshen wadannan matsalolin?

ADENIJI: Ko da yake wannan kungiya bata da iko ko karfin ganin cewa fannin kiwon lafiya ta samu yadda ta ke so, tana iya kokarinta wajen ganin cewa gwamnati ta samar wa fannin da ma’aikatanta duk abubuwan da suke bukata a iya karfinta.

PT: Menene kungiyar NANNM ke yi akan masu taimakawa ma’aikatan jinya da ake basu iko wasu lukutta wajen kula da majinyata.

ADENIJI: Duk irin wadanan abubuwa ne kungiyar mu ke kokarin kauda wa a asibitocin kasar nan. Bamu yarda da irin wadannan ma’aikata ba kuma barinsu suna wuce iyakansu ya kan zama hadari ga majinyata, amma muna kokarin ganin cewa an kau da hakan a asibitocin sannan kuma mu kara wayar da kan dukkan ma’aikatan asibiti domin kowa ya san inda aikin sa ya fara da kuma inda ya kare.

Sannan kuma duk wanda aka samu yana aikin da ba nasa ba ko kuma ba kwararre bane a aikin sa kungiyar zata hukuntashi, in ya kama a daure shi za mu tabbatar anyi hakan.

PT: Bincike ya nuna cewa Mata ne suka fi zama ma’aikatan jinya wato ‘Nurses’ Menene kungiyar NANNM ta ke yi domin ganin cewa maza sun kara yawa a aikin?

ADENIJI: Muna kokarin ganin mun dada wayar da kan maza je domin su dauki sana’ar aikin kula da majinyata da mahimmanci.

Share.

game da Author